Cibiyar Wayar Da Kan Jama’a da sanya ido kan ayyukan Majalisar Dokoki da yaƙi da cin hanci da rashawa (CISLAC) ta yi kira ga majalisar tarayya, jami’an tsaro da gwamnatin tarayya da su sake duba jerin mutanen da ake shirin naɗawa a matsayin Jakadu tare da kin amincewa da nadin Ayodele Oke daga jihar Oyo a matsayin jakada marar sana’a saboda zarge-zargen cin hanci da ke kansa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutane uku da aka zaba a matsayin jakadu marasa a ranar Laraba da suka haɗar da Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga jihar Jigawa da Ayodele Oke daga jihar Oyo.
Wannan buƙata ta biyo bayan fiye da shekaru biyu da janye dukkan jakadun Najeriya da gwamnati ta yi a watan Satumbar shekarar 2023.
CISLAC ta bayyana matuƙar damuwa kan yadda Ayodele Oke, wanda hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziƙi kasa ta’annati EFCC ta ayyana shi, shi da matarsa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo saboda manyan zarge-zargen rashawa, ya kasance cikin jerin mutanen da aka zaɓa zuwa muƙamin diflomasiyya mai matuƙar muhimmanci.
Ayodele Oke, wanda ya taɓa zama darakta janar na hukumar leken asiri ta ƙasa NIA, an ayyana shi a matsayin wanda ake nema bayan ya kasa bayyana a gaban kotu domin fuskantar tuhumar zamba da ake yi masa.
A ranar 7 ga Fabrairu 2019, mai shari’a Chukwujeku Aneke na babbar kotun tarayya da ke Legas ya bayar da umarnin kama Ayodele Oke da matarsa bayan hukumar EFCC ta gabatar da bukata ta hannun lauyanta Rotimi Oyedepo.
Ma’auratan suna da alaƙa da tarin kuɗaɗen da suka haɗa da dala 43,449,947 da fam 27,800 da kuma naira 23,218,000 da aka gano a wani gida da ke titin Osborne a Ikoyi, Legas a watan Afrilu 2017.
Dangane da wannan lamari, Daraktan CISLAC kuma shugaban kungiyar Transparency International a Najeriya, Comrade Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani, ya bayyana nadin a matsayin abin damuwa da kunya, da kuma nuna rauni ƙwarai ga ƙudurin Najeriya na gaskiya, da ɗaukar alhakin aiki da yaƙi da rashawa.
Ya nuna cewa nadin irin wannan mutum na iya raunana aikin hukumomin yaƙi da rashawa.
A cewarsa, duk lokacin da ake amincewa da mutanen da ake bincike a kan su zuwa muƙaman siyasa, hakan na rage ƙoƙarin EFCC, ICPC da sauran hukumomin yaƙi da rashawa.
A cewar CISLAC, akwai bukatar majalisar dattawa da sauran hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan bayanan waɗanda ake shirin naɗawa domin tabbatar da cewa ba su da alaƙa da ayyukan da suka saba wa doka ko manufofin yaƙi da cin hanci.
Kungiyar ta ƙara da cewa gwamnati na da nauyin tabbatar da cewa duk wanda zai samu muƙami ba shi da wani hani ko rahoto daga hukumomin bincike, domin kauce wa sanya mutanen da za su iya gurgunta ƙoƙarin yaƙi da rashawa da ingantaccen mulki.
CISLAC ta jaddada cewa kare mutuncin muƙaman gwamnati da tabbatar da tsabtace tsarin nadin shugabanni na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da gaskiya, adalci da martaba ga al’ummar Najeriya.













































