Shugaban kwadago ya rasu a wajen taron kwadago na duniya a Geneva

Mike Adeleke

Wakilan Najeriya a taron ‘yan kwadago na duniya (ILC) karo na 114 a Geneva da daukacin ‘yan kwadago baki daya sun shiga cikin alhini bayan mutuwar shugaban kwadago Domingo Michael Adeleke.

Adeleke, wanda shi ne shugaban Majalisar Tattaunawa ta Hadin Gwiwa ta Jihar Lagos (JNC), ya rasu a ranar Talata a Geneva bayan gajeriyar rashin lafiya.

Ya je kasar Switzerland ne a matsayin guda cikin wakilan Najeriya a taron lokacin da aka ce ya kamu da rashin lafiya sannan daga nan aka kai shi asibiti, yayin da ya rasu daga baya.

Wani jami’in Kungiyar Kwadago ta Kasa( NLC) ne ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana Adeleke a matsayin mai fafutukar kwadago da ya sadaukar da kansa wajen jin dadin ma’aikata.

“Cikin bakin ciki, Kungiyar Kwadago ta Kasa da ta ‘yan kasuwa baki daya a Najeriya, musamman Wakilan Ma’aikata a Taron Kwadago na Duniya na 2026, ke sanar da rasuwar Comrade Domingo Michael Adeleke, wanda ya rasu a yau a Geneva bayan gajeriyar rashin lafiya yayin halartar taron ILC na 114,” in ji jami’in.

Adeleke, memban Kungiyar Ma’aikatan Gwamnati ta Kasa (NCSU), ya yi aiki a matsayin shugaban Majalisar Tattaunawa ta Hadin Gwiwa ta Jihar Lagos, inda ya shiga fafutukar kare hakkin ma’aikata da shirye-shiryen jin dadinsu.

A cewar NLC, ya ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta aikin yi mai kyau da adalcin zamantakewa a duk tsawon aikinsa.

“Rasuwarsa ta shafi duk wadanda suka san shi da kuma wadanda suka yi aiki tare da shi,” in ji jami’in.

NLC ta ce shugabancinta sun ziyarci asibitin da aka ajiye gawarsa kuma sun fara shirye-shiryen dawo da ita zuwa gida.

Ana ci gaba da karbar ta’aziyyoyi daga shugabannin kwadago da ma’aikata wadanda suka tuna Adeleke saboda gudummawarsa ga harkar kwadago da jin dadin ma’aikata.

NLC ta mika ta’aziyyarta ga iyalansa, abokan aikinsa da mambobin kungiyar kwadago, inda ta bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.

“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, NLC da daukacin masu fafutuka a fadin Jihar Lagos. Allah ya jikan sa, kuma sadaukarwarsa ga hakkokin ma’aikata ta ci gaba da zama abin koyi a gare mu,” in ji kungiyar.

Abokan aikinsa suna tunawa da Adeleke a matsayin mai fafutukar kwadago mai sadaukarwa wanda ya sadaukar da mafi yawan rayuwarsa ga aikin gwamnati da cigaban muradun ma’aikata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here