Jakadan Najeriya a kasar Rasha Abdullahi Shehu, ya ce gwamnatin tarayya na nazarin hanyoyin da za ta farfado daya daga cikin manyan kadarorin kamfanin karafa na Ajaokuta dakuma gayyatar masu zuba jari daga kasar Rasha.
Shehu ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a birnin Moscow, inda ya bayyana cewa a ko da yaushe Rasha abokiyar kawancen Najeriya ce.
Shehu ya ce farfado da kamfanin karafa na Ajaokuta na daya daga cikin manufofin wanna tattaunawa tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaran sa, Vladimir Putin na Rasha, a lokacin gangamin taron kasashen Afirka da Rasha na farko a birnin Sochi na kasar Rasha, a shekarar 2019.
Ya ce duk da cewa Kamfanin Rasha a karkashin Tarayyar Soviet a lokacin ya gina masana’antar Karfe har sama da kashi 90 cikin 100 kafin su tashi a shekarar 1983, amma gwamnatin tarayya na da duba dabaru kan yadda za a farfado da kamfanin.
Kamfanin dillacin labran Najeriya ya rawaito cewa, a yayin da Najeriya ke kokarin farfado da tattalin arzikinta da kuma ficewa daga kasa mai dogaro da man fetur, gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake gyara wasu sassan tattalin arzikin kasar.











































