Wasu yan Daba sun farmaki jirgin yaƙin neman zaben Olajide Adediran, ɗan takarar gwamnan jihar Legas karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2023.
A wata sanarwa da shugaban PDP reshen Legas, Hakeem Amode, ya fitar, yace an farmaki Adediran wanda aka fi sani da Jandor a yankin Ikoga junction, ƙaramar hukumar Badagary ranar Lahadi.
Amode ya bayyana cewa mutane da yawa dake cikin tawagar sun jikkata sakamakon harin cikinsu har da yan jarida, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
“Yan Daban da APC ta ɗauki nauyi sun kai hari ga ayarin kamfen ɗan takarar gwamnan PDP a hanyar dawowa daga ziyarar mambobin jam’iyya a Ikoga junction, ƙaramar hukumar Badagary.”
“Harin ya yi sanadin raunata da yawan mambobin tawagar Jandor da manema labarai. A yanzu haka akawai ɗan jaridar da ke cikin mawuyacin hali a wani Asibiti yayin da aka yi wa sauran maganin raunukansu.”
“Maharan da suka farmaki ayarin kamfen sun bude wuta suna kiran APC kana sun yi amfani za muggan makamai. Idan baku manta ba mun yi zargin APC na shirin amfani da yan daba don kai hari ga ɗan takararmu, Jandor.”













































