Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta’addanci a Najeriya 

05013be291a25879
05013be291a25879

Rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata da masaniya kan gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya yi a Najeriya game da yuwuwar kai hari babban birnin tarayya Abuja.

Da yake martani ga tambayar da jaridar Leadership tayi masa a jiya Lahadi, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce bai da masaniya kan kowani barazana na tsaro.

Da aka tambaye shi game da shirin yan sanda na dakile harin, kakakin rundunar wanda bai zurfafa magana kan lamarin ba, ya amsa tambayar a takaice da “bani da masaniya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here