Dantakarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace shirya-shirye sun yi nisa domin naɗa tawagar kamfen ɗinsa.
A wata hira da sashin Hausa na BBC, Kwankwaso ya bayyana cewa yaƙi sanar da manufofinsa ga ‘yan Najeriya ne domin gujewa yuwuwar sata daga wasu jam’iyyu.
“Zamu sanar da tsarin mu da manufofinmu da kuma hanyar da zamu bi wurin aiwatar da su. Kuma na mu zai banbanta da na sauran ‘yan takarar shugaban kasa.”










































