Ba mu da wani shiri na cire shugaban hukumar zabe- Fadar shugaban kasa

INEC INEC 2
INEC INEC 2

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rade-radin da ake na shirin tsige Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da kuma dakatar da amfani da tsarin amfani da na’urar zabe BVAS a babban zaben 2023.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Mista Femi Adesina ya bayyana haka a wani shirin tattaunawa kan manufofin da aka shirya domin tunawa da ranar kawo karshen cin zarafin ‘yan jarida ta duniya na shekarar 2022 a Abuja.

Adesina ya shawarci ‘yan jarida da kada su biyewa masu boye aniyar kawo cikas a zaben 2023 ta hanyar yada jita-jita.

“Kwanan nan, akwai wata kungiya da ta ce akwai alamun za a tsige shugaban hukumar ta INEC saboda kila ba sa son amfani da na’urar BVAS mai dakile duk wata hanyar magudi.

“Sai da fasaha ta zo aka samu katin zabe na dindindin don haka abune mai wuya a rubuta sakamako.

Adesina ya ce a ranar Litinin din da ta gabata ne Buhari a wani taro a jihar Imo, ya kuma baiwa ‘yan sanda umarnin tabbatar da zaben 2023 cewa zai zamo mai inganci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here