Gwamnatin tarayya ta damƙa aikin noman Gari mai faɗin Hekta 228 ga manoma a jihohin Jigawa da Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Misis Oyeronke Oluniyi, Darakta a ma’aikatar noman rani da kula da madatsun ruwa ta ma’aikatar ruwa ta miƙa kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Abuja ya ruwaito yau Alhamis.
“Misis Oyeronke Oluniyi, ta mika ragamar aikin ne a madadin Ministan gona Malam Suleiman Adamu.
Oluniyi ya ci gaba da cewa: “Kananan hukumomi biyar da suka haɗa da Kazaure da Roni a Jigawa da Kunchi da Dambatta da Makoda a Jihar Kano, a karkashin Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama’are ne ke cin gajiyar aikin.
Ta ce aikin wani bangare ne na samar da abinci da ayyukan yi da gwamnati ke yi.
Oluniyi ya ce aikin ban ruwa, wanda aka kai wa manoma a sassa yana cikin kashi na shida, biyo bayan shawarar da gwamnati ta yanke na kammala dukkan ayyukan don samun fa’ida mai yawa.
Ta ce ma’aikatar, bisa aikinta na noman ban ruwa, ta yi daidai da manufofin gwamnati mai ci na habaka tattalin arzikin kasa tare da fitar da mutane da dama daga kangin talauci kafin shekarar 2030.













































