Yar Najeriya ta zama Birgediya Janar a rundunar sojin Amurka

Brigadier General Amanda Azubuike 2 750x430 1
Brigadier General Amanda Azubuike 2 750x430 1

Wata mace ‘yar asalin Najeriya mai suna Amanda Azubuike ta samu Karin girma daga mukamin Laftanar Kanal zuwa mukamin Birgediya Janar a rundunar sojin Kasar Amurka.

Amanda Azubuike, wacce zuriyarta ke da alaka da Najeriya, ta samu sabon mukamin ne a yayin wani bikin da aka gudanar na wani rukunin sojoji da ke Fort Knox dake Kentucky, a Amurka.

Wani babban kwamanda na rundunar sojin Amurka Janar James Rainey, ya ce bisa Irin jagorancin Azubuike da ta yi kowa da ya kasance a karkashin ta ya gamsu da salon jagorancin ta.”

Azubuike, Yar kasar Amurka, iyayen ta ne, ‘Yan Najeriya, Kuma suka haife ta a birnin Landan na kasar Ingila.

Tun a Shekarar 1994 ta shiga kwalejin horas da Jami’an Jiragen Sama na Sojoji.

Kafin ta koma aikin Soja a matsayin jami’ar hulda da jama’a, ta yi aiki a bangaren sufurin jiragen sama na tsawon shekaru 11.

Amanda Azubuike ta taba rike mukamin Mai bada shawara ga babban hafsan sojoji, a ofishin sakataren tsaro.

A halin yanzu, dai ta kasance mataimakiyar kwamanda a Rundunar Sojojin Amurka.

A baya ta rike mukaman Daraktar Hulda da Jama’a a shiyyar Washington da Kuma shugabar sashen Hulda da Jama’a a Rundunar Kudancin Amurka wato yankin Fort Lauderdale.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here