Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dage tafiyarsa da aka tsara zuwa birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu da kuma Luanda a ƙasar Angola, domin jiran samun ƙarin bayanan tsaro kan daliban makarantar mata da aka sace a Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada na cocin Christ Apostolic Church a Eruku, Jihar Kwara.
Wannan na cikin sanarwar da Bayo Onanuga mai bawa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare ya fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, wannan na matsayin amsa bukatar gwamnan Jihar Kwara da Shugaba Tinubu ya yi, har ma ya umurci a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa garin Eruku da dukan yankin ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar, tare da umartar rundunar ƴan sanda ta bi diddigin ƴan bindigar da suka kai wa masu ibada hari.
Shugaban ƙasa Tinubu ya shirya barin Abuja a Laraba domin halartar babban taron shugabanni na G20 karo na ashirin a Afirka ta Kudu, sannan daga nan ya wuce zuwa Luanda domin halartar taron ƙungiyar Tarayyar Afirka AU da ƙungiyar Tarayyar Turai EU karo na bakwai.
Karanta:
Tinubu zai tafi Afrika ta Kudu da Angola a ranar Laraba
Yanzu haka Shugaba Tinubu yana jiran rahotannin da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai gabatar masa bayan ya kai ziyarar jaje a Kebbi a madadinsa, da kuma rahotannin da ƴan sanda da hukumar tsaro ta DSS za su mika masa kan lamarin da ya faru a Kwara.
Shugaban ƙasa Tinubu ya sake nanata umarninsa ga hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen ceto dalibai mata 25 da ƴan bindiga suka sace, tare da dawo da su gida lafiya.











































