Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 da ya kai Naira Tiriliyan 1.368,127,929,271 ga majalisar dokokin jihar a ranar Laraba.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, wanda ya bayyana tsarin rabon kuɗaɗen cikin kasafin.
Sanarwar ta nuna cewa kaso Sittin da Takwas cikin Ɗari na kuɗaɗen an ware su ne domin gudanar da manyan ayyuka wanda ya kai Naira Biliyan Ɗari Tara da Talatin da Huɗu da Miliyan Ɗari Shida, yayin da kaso Talatin da Biyu cikin ɗari da ya kai Naira Biliyan Ɗari Huɗu da Talatin da Uku da Miliyan Ɗari Huɗu, aka warewa bangaren gudanarwa.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa tsarin rabon kuɗaɗen ya dace da muhimman fannoni na ci gaban jihar, inda fannin ilimi ya sami kaso na Naira Biliyan Ɗari Huɗu da Biyar da Miliyan Ɗari Uku, fannin manyan ayyuka ya sami kaso na Naira Biliyan Ɗari Uku da Arba’in da Shida da Miliyan Ɗari Biyu, sannan fannin lafiya ya sami kaso na Naira Biliyan Ɗari Biyu da Goma sha Biyu da Miliyan Ɗari Biyu.
Ya kuma bayyana cewa sauran muhimman fannoni kamar noma, tsaro, kasuwanci, ruwa, muhalli, yawon buɗe ido, ci gaban mata da matasa, da kuma mutanen da ke da bukatu na musamman, sun samu muhimman tanade-tanade a cikin kasafin.
Gwamnan ya bayyana kasafin kuɗin a matsayin tsari mai ƙarfi da manufa, wanda aka yi domin aiwatar da muhimman ayyuka da hidimomi da za su dace da muradun jama’ar jihar.
Ya roƙi majalisar Dokokin ta hanzarta amincewa da kudurin, yana mai jaddada cewa aikin majalisa na duba kasafi da yin haɗin gwiwa yana da muhimmanci wajen juya waɗannan tsare-tsare zuwa amfanin kai tsaye ga al’umma.
Kasafin kuɗin Naira Tiriliyan 1.368 ya zama babban ci gaba a tarihin jihar, domin ya haura duk wani kasafin manyan ayyuka da wata jiha a Arewa ta taɓa gabatarwa a baya.













































