Zargin ta’addanci: Buratai ya maka Ali-Keffi a kotu yana neman diyyar Naira Biliyan Ɗaya kan ɓatanci

Tukur Buratai 750x430

Tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai mai ritaya, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna kan wani tsohon babban jami’in soja, Manjo Janar Danjuma Hamisu Ali-Keffi mai ritaya, yana neman a ba shi diyyar Naira Biliyan Ɗaya bisa zargin ɓatanci da alaƙanta shi da ayyukan ta’addanci.

Ƙarar ta ta’allaka ne kan zargin cewa Ali-Keffi ya yaɗa kalamai da ake ganin ƙarya ne, masu cutarwa da kuma mummunan nufi, waɗanda suka danganta Buratai da tallafa wa ta’addanci, zargin ’yan Boko Haram, da kuma zargin saki ko ɓoye waɗanda ake zargi da ta’addanci ba bisa ka’ida ba.

A cikin takardun ƙara da lauyoyin Buratai suka shigar, an nemi kotu ta ayyana cewa kalaman da ake jingina wa wanda ake ƙara, waɗanda aka wallafa a jaridu na labarai da na sada zumunta ciki har da Sahara Reporters da wasu kafafe, ɓatanci ne kuma sun yi mummunar illa ga mutuncin Buratai.

Takardun kotu sun nuna cewa Buratai ya zargi Ali-Keffi da bayar da hirarraki a baya inda ya nuna tamkar tsohon babban hafsan sojin yana da alaƙa da masu ta’addanci da masu ɗaukar nauyinsu, tare da shiga shirye-shiryen ɓoye ayyukan ta’addanci a lokacin da yake rike da mukamin babban hafsan sojin ƙasa.

Labari mai alaƙa: Buratai ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan jaridar Internet da wani Janar mai ritaya kan danganta shi da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci

Buratai ya bayyana cewa wallafe-wallafen sun samu yaduwa sosai a dandalin sada zumunta da kafafen yaɗa labarai, lamarin da ya ba zarge-zargen damar kaiwa matakin ƙasa da ma ƙasashen waje, wanda Buratai ya ce ya jawo masa mummunar illa ga sunansa da mutuncinsa.

Buratai ya jaddada cewa zarge-zargen ba su da tushe, yana mai cewa bai taɓa fuskantar bincike, tuhuma ko hukunci kan ta’addanci ko tallafa wa ta’addanci ba, kuma ya ce wallafe-wallafen sun nuna shi a matsayin mai cin hanci, marar kishin ƙasa da kuma mai taimaka wa ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Saboda haka, ya nemi kotu ta umurci Ali-Keffi da janye kalaman da ake zargin ɓatanci ne tare da wallafa neman afuwa ga jama’a ba tare da sharadi ba a Sahara Reporters, aƙalla jaridu biyu na ƙasa da kuma dukkan dandalin da aka yaɗa kalaman, tare da ba da umarnin hana maimaita irin waɗannan kalamai a gaba.

Bugu da ƙari, Buratai yana neman diyyar Naira Biliyan Ɗaya a matsayin diyya ta gaba ɗaya kan ɓatanci, da kuma umarnin kotu na dindindin da zai hana Ali-Keffi sake wallafawa ko maimaita irin waɗannan kalamai, tare da biyan dukkan kuɗaɗen shari’a.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa har yanzu ba a saka ranar fara sauraron shari’ar ba kuma wanda ake ƙara bai gabatar da martani ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here