Tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya yi barazanar daukar matakin shari’a kan jaridar Internet ta Sahara da Janar Manjo Danjuma Ali-Keffi mai ritaya kan abin da ya kira zarge-zarge marasa tushe da suka danganta shi da daukar nauyin ayyukan ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadinsa ta hannun Birgediya Janar Sani Usman mai ritaya a ranar Asabar a Abuja, Buratai ya ce zargin an kirkire shi ne domin bata masa suna, domin kuwa labarin ya dogara kacokan kan ikirarin Ali-Keffi ba tare da wata hujja ta zahiri ko ta shari’a ba.
Ya bayyana cewa a duk tsawon aikinsa ba wani hukumomin tsaro ko na leken asiri ko kwamitocin bincike da suka taba tuhumarsa ko bincikarsa kan batun kuɗaɗen ta’addanci, don haka danganta shi da hakan ba shi da wata hujja.
Buratai ya kuma zargi jaridar Sahara da yaɗa farfaganda a kansa, yana mai cewa dukkan yunƙurin da aka yi a baya domin bata masa suna ya ci tura ne saboda tarihin aikinsa ya kasance mai gaskiya, bayyananne kuma abin koyi.
Karanta: Tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya Malami ya musanta zargin tallafawa ayyukan ta’addanci
Ya ce fiye da shekaru arba’in na hidimar soja da ya yi sun kasance cike da jarumta da kwareqa da jajircewa wajen yakar Boko Haram da ISWAP, inda a zamaninsa sojojin ƙasa suka kwato yankuna, suka dawo da ikon gwamnati, tare da mayar da mutanen da suka rabu da muhallansu.
Buratai ya nemi jaridar Sahara da Ali-Keffi su janye zargin tare da bada hakuri a fili, in ba haka ba zai dauki matakin shari’a don kare mutuncinsa.
Buratai ya ce, yanzu ya mayar da hankali ne kan bincike, tattaunawar manufofi, aikin zaman lafiya da ayyukan jin-kai, kuma ba za a rushe gadon aikinsa ta hanyar yada bayanan karya ba.
NAN













































