Tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Ologbondiyan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, tare da wasika mai dauke da kwanan wata 5 ga Disamba 2025 da ya aika wa shugaban mazabar Okekoko (09), a karamar hukumar Kabba/Bunu ta jihar Kogi.
A cikin wasikar da ya yiwa take da “Sanarwar janye zama ɗan jam’iyya”, Ologbondiyan ya ce bayan nazari kan rawar da ya taka a cikin PDP, ya yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zai bar jam’iyyar saboda dalilai na kansa.
Ya kara da cewa ya yanke hukuncin janye zaman sa cikakken memba daga PDP daga wannan lokaci, sannan ya gode wa jagorancin jam’iyyar bisa damar da suka ba shi na yi wa jam’iyyar da kasa hidima.
Ficewar tasa na daga cikin jerin manyan jami’an da suka bar PDP a shekarar 2025, wadda ta kasance daya daga cikin shekarun da jam’iyyar ta fuskanci kalubale masu tsanani tun kafuwarta.












































