Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta ki shiga muhawara a bainar jama’a kan matakin ladabtarwa da ta dauka a kan Mukaddashin Daraktan Watsa Labarai da Kididdiga na Kotun Daukaka Kara ta Shari’a ta Jihar Kano, Ado Muzambilu. Ta ce lamarin yanzu yana gaban kotu mai hurumin sauraron, don haka ya kamata a ba ta damar da ta dace.
SolaceBase ta ruwaito cewa matsayar hukumar na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’arta, Baba Jibo Ibrahim ya fitar a ranar Talata. In da ya ce wannan bayani ne saboda rahotannin kafofin watsa labarai da sharhin jama’a da suka biyo bayan matakin ladabtarwa da aka dauka a kan Muzambilu da kuma karar da ya shigar a gaban kotu.
A cewar sanarwar, JSC tana matukar girmama tsarin doka da ‘yancin cin kashin kai na shari’a, don haka ba za ta shiga gardama da kowa ba kan wata matsala da ke gaban kotu a yanzu.
“Hukumar ta ga ya zama dole ta bayyana cewa ba za ta shiga muhawara a bainar jama’a ko shiga gardama da kowanne bangare ba kan wata matsala da ke gaban kotu mai hurumin yanke hukunci a yanzu,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce an dauki matakin ladabtarwa kan Muzambilu ne bisa cikakken aiki da hurumin da kundin tsarin mulki da doka suka ba ta.
Ta bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan nazarin dukkan hujjoji da bayanan da aka gabatar mata, kuma ya yi daidai da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Ka’idojin Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a, Dokokin Aikin Gwamnatin Jihar Kano da sauran dokokin da suka shafi ladabtar da jami’ai da ma’aikatan shari’a da ke karkashinta.
Ta kuma sake jaddada kudirinta na kiyaye mutunci, aminci da alhakin da ke kan bangaren shari’a, tana mai cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kundin tsarin mulki cikin adalci, gaskiya, ba tare da son kai ba, kuma ba tare tsoro ba.
Yayin da ta ki yin wani bayani a kan lamarin, hukumar ta ce yin hakan na iya cutar da shari’ar da ke gudana.
Saboda haka ta bukaci jama’a da kafafen yada labarai da su guji yin hasashe da yawa tare da ba kotu damar yanke hukunci kan batun.












































