Jam’iyyar NDC ba ta da dan takarar gwamna har yanzu a Jihar Kaduna a zaben 2027- Shugaba

NDC NDC

Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa har yanzu ba ta tsaida dan takarar gwamna ba a zaben 2027 a Jihar Kaduna, duk da takaddamar da ke tsakanin tsohon Sanata Danjuma La’ah da Barista Mohammed Abbas.

Shugaban jam’iyyar na jiha, Evangelist Mordecai Ibrahim, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya jaddada cewa dambarwar da ake yi kan tikitin gwamnan jam’iyyar ba ta riga ta kau ba.

Ibrahim ya bayyana cewa dole ne jam’iyyar ta gudanar da zaben fitar da gwani na maida gurbi kafin ta samu halataccen dan takara, bayan da shi kansa ya janye daga takarar.

Ya ce, “Gaskiya mai daci ita ce, ko a matakin jiha ko na kasa, ba a riga an yanke shawarar wane ne takamaiman dan takarar gwamnan Jihar Kaduna ba tsakanin Barista Mohammed Sani Abbas ko Sanata Danjuma Tellah La’ah ba.”

Shugaban ya bayyana cewa shi ne halataccen dan takara wanda hukuma ta sani tun farko har sai lokacin da ya yanke shawarar janyewa da kansa.

A cewarsa, ya aike da takardar sanarwa ga Shugaban Jam’iyyar NDC na Kasa da kuma Kwamishinan Zabe na Jihar Kaduna (REC) don sanar da janyewarsa kamar yadda Sashi na 31 na Dokar Zabe ta shekarar 2026 ya tanada.

Ibrahim ya ce ya mika takardar janyewar mai kwanan wata 7 ga watan Agusta, wadda aka karba a ofishin shugaban na kasa, tare da rantsuwar kotu da ke goyon bayan matakin nasa.

Ya kuma nuna takardar takaitaccen bayani na hukumar INEC game da mutanen da jam’iyyu daban-daban suka tsayar a zaben 2027, inda sunansa ke ciki a matsayin dan takarar gwamna na NDC.

Wannan al’amari ya haifar da sabuwar dambarwa kan wanda zai gaji tikitin jam’iyyar, yayin da La’ah da Abbas ke ikirarin su ne ya kamata a mika wa takarar.

Wani bangare na jam’iyyar ya musanta cewa an baiwa La’ah tikitin takarar gwamnan.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NDC na Kasa, Shiyyar Arewa, Alhaji Sidi Bomi, an ruwaito ya yi watsi da wata takarda da ke yawo a kafofin sada zumunta mai dauke da sunan La’ah.

Bomi ya ce takardar ba ta fito daga jam’iyyar ba, saboda haka kada a dauke ta a matsayin hujja da ke nuna La’ah ne dan takarar NDC.

A daya bangaren, Abbas ya ci gaba da jaddada cewa shi ne halataccen dan takarar gwamna na jam’iyyar.

Sai dai shugaban jam’iyyar ya yi watsi da wannan ikirarin, inda ya zargin Abbas da yin karya na cewa ya shiga zaben fidda gwani kuma ya yi nasara.

“Abin takaici ne kwarai ga masanin shari’a ya rika fadar irin wannan Magana ta karya cewa ya shiga zaben fidda gwani kuma ya yi nasara, alhali ya san karya ce tsagwaranta. Babu abin da za iyi nesa da gaskiya kamar wannan da’awar ta rashin gaskiya.”

Ibrahim ya ce jam’iyyar ba za ta iya magance wannan takaddama ta hanyar farfaganda ko ikirarin baki ba, yana mai cewa dole ne a bi tsarin zabe na cikin gida da ya dace.

Ya bayyana cewa, “Bisa tanadin Sashi na 31 na Dokar Zabe ta 2026, yanzu jam’iyyar NDC tana da zabin shirya zaben fitar da gwani na mayar gurbi kawai domin halataccen dan takara ya fito tun da ba su iya cimma matsaya na bai-daya ba – saboda haka duk wani abu da ba wannan ba zai zama haramtacce.”

Haka zalika, shugaban ya bayyana cewa wasu ‘yan takara biyu, Zariyi Madaki da Ibrahim Abdulkarim, sun janye daga takarar domin marawa La’ah baya a taron neman maslahar farko da aka yi a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Ya bayyana La’ah a matsayin dan siyasa mai gogewa, inda ya bayyana cewa tsohon sanatan ya yi wa’adi biyu kuma a wani lokaci shi kadai ne sanatan PDP a Jihar Kaduna da daukacin shiyyar Arewa maso Yamma.

Duk da haka, Ibrahim ya shauri Abbas da ya mayar da hankali wajen gina tsarin siyasarsa a matakin mazabu da kananan hukumomi.

Ya ce, “Kowane dan siyasa nagari zai fara tabbatar da cewa mazabarsa da karamar hukumarsa suna bayansa domin ai alheri daga gida yake farawa.”

Sanarwar ta shugaban ta kara rura wutar rikicin cikin gida na jam’iyyar NDC a Jihar Kaduna yayin da jam’iyyar da ‘yan takara ke shirin fafatawa a zaben gwamna na shekarar 2027.

Membobin Kwamitin Aiki na Jam’iyyar a Jihar Kaduna, da suka amince da wannan sanarwa, ciki har da Shugaban NDC na Shiyyar Kudancin Kaduna Obed Danjuma, Shugaban Shiyyar Tsakiyar Kudancin Kaduna Aminu Idris, Mataimakin Sakataren Jiha Emmanuel Dogara, Shugabar Mata ta Jiha Ruth David, Mukaddashin Sakataren Tsare-tsare Ibrahim Yunusa, Masu Ba da Shawara Kan Shari’a Barnabas John, Odita Micah Ayuba, Ma’aji Ayuba Yashim, Sakataren Jin Dadin Jama’a: Gideon Nuhu, Shugaban Karamar Hukumar Chikun kuma Shugaban ALGON Kwamanda Bitrus Yahaya da Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari kuma Sakataren ALGON Sabiu Ibrahim.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here