Tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Kenneth Okonkwo ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar, saboda rikicin shugabancin cikin gida da kuma rashin alkibla.
Okonkwo wanda ya taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar LP a shekarar 2023, ya ce ya dauki matakin ne sakamakon gazawar jam’iyyar wajen tabbatar da shugabanci na gari, wanda shi ne babban dalilinsa na shiga harkokin siyasa.
Fitaccen dan wasan Nollywood wanda ya koma siyasa ya bayyana cewa LP, a halin da take ciki, “ba ta da makoma” kuma ba za ta iya biyan bukatun ‘yan Najeriya ba.
Karanta har ila yau: Kwamitin binciken rikicin siyasar Kano ya yi alkawarin yin adalci
Tafiyar Okonkwo ita ce ta baya-bayan nan a cikin jerin rigingimu da suka dabaibaye jam’iyyar Labour a ‘yan kwanakin nan, har ma aka jiyo shi ya soki shugaban jam’iyyar na kasa Julius Abure, inda ya zarge shi da fifita bukatun kashin kansa fiye da na jam’iyyar.
A cewar Okonkwo, wa’adin shugabancin jam’iyyar LP ya kare tun da dadewa, inda ya kara da cewa yunkurin ceto jam’iyyar ta hanyar kwamitin rikon kwarya ya samu cikas ta hanyar shari’a.
Rashin gamsuwarsa da jam’iyyar ba sabon abu ba ne, inda ko a cikin watan Yuni 2024, ya bayyana LP a matsayin “ƙungiyar matsala wacce gungun marasa kishi ke jagoranta.”