Tinubu Ya Kori Ministoci 5 Ya Nada Sabbin Mataimaka

president bola ahmed tinubu 750x430

A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Tinubu ya kori ministocinsa biyar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ya fitar ranar Laraba.

Shugaban kasar ya kori Uju-Ken Ohanenye a matsayin ministar harkokin mata; Lola Ade-John a matsayin ministar yawon bude ido; Tahir Mamman a matsayin Ministan Ilimi; Abdullahi Gwarzo a matsayin karamin ministan gidaje da raya birane; da Jamila Ibrahim a matsayin ministar ci gaban matasa.

“Nadin Shehu Dikko a matsayin shugaban hukumar wasanni ta kasa.
“Nadin Sunday Akin Dare a matsayin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan sadarwa da wayar da kan jama’a da ke aiki daga ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here