Gwamnatin Kano ta haramta yin Muƙabala tsakanin Sha’irai ba tare da izini ba, ta umarci wasu Sha’iran su bayyana gabanta

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430 (1)

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da dukkan Muƙabalar Sha’irai da ake gudanarwa a jihar ba tare da samun sahalewar hukumar ba.

Sakataren gudanarwa na hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar Talata.

Ya ce matakin ya zama dole ne domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin nishaɗi da addini.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon wata Muƙabala da aka gudanar ba tare da amincewa ba tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi, abin da ya saba wa ƙa’idojin aiki na hukumar.

A cewar sanarwar, an kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Daraktan harkoki na musamman a hukumar, Malam Isha Abdullahi, domin gudanar da bincike kan lamarin.

Haka kuma, an ba wa Sha’iran biyu da masu gudanar da Muƙabalar wa’adin sa’o’i 24 su bayyana gaban kwamitin.

Hukumar ta jaddada cewa shirya irin waɗannan Muƙabalar ba tare da izini ba ya karya dokar tace fina-finai ta jihar Kano, kuma hakan na iya jawo hukunci mai tsanani daga doka.

El-Mustapha ya nanata kudirin hukumar na ci gaba da kula da harkokin Sha’irai da masu rera waƙoƙi a jihar cikin bin doka.

Ya roƙi al’umma da su kwantar da hankula tare da bayar da goyon baya ta hanyar ba da sahihan bayanai da za su inganta zaman lafiya da cigaban al’adu a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here