Hukumomin kasar Libiya sun mika ‘yan Najeriya 18 da ba su da takardun zama daga cibiyar tsare baki ta Sirte zuwa garin Sabha da ke kudu, inda ake sa ran za a mayar da su Najeriya a cikin kwanaki masu zuwa.
Kungiyar agaji ta Migrant Rescue Watch ce ta tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, inda ta bayyana cewa an yi jigilar ne ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar yaƙi da shige da fice ta Libiya (DCIM).
Kungiyar ta ce an kai mutanen ne cikin rakiyar jami’an tsaro, a wani ɓangare na tsarin Libiya na mayar da bakin da ke zaune ba bisa ƙa’ida ba zuwa kasashensu.
Rahoton ya nuna cewa waɗannan mutanen an kama su ne a yayin ƙoƙarin tsallaka zuwa Turai ta haramtacciyar hanya.
Za su ci gaba da kasancewa a cibiyar tsare baki ta Sabha har sai an kammala shirye-shiryen mayar da su Najeriya.
Karanta: DSS ta kai Sowore, kamfanin X da Meta kotu
Kasashen duniya da dama sun sha bayyana damuwa kan cunkoson jama’a, rashin ingantattun yanayi da kuma cin zarafi da ake fuskanta a irin waɗannan cibiyoyin tsare baki na Libiya.
Duk da rikice-rikicen siyasa da yaƙe-yaƙe da suka daɗe suna addabar Libiya, kasar na ci gaba da zama babban hanya ga ‘yan gudun hijira da ke ƙoƙarin ketarawa Turai ta Tekun Bahar Rum.
A ‘yan shekarun baya, Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta yi haɗin gwiwa da hukumomin Libiya wajen shirya jigilar su na son rai domin ba su damar komawa kasashensu cikin aminci.












































