Hukumar Zaben Najeriya INEC ta yi watsi da bukatar gamayyar jam’iyyun siyasar da suka yi rajista, (IPAC) ta neman karin lokacin gudanar da zabukan fidda gwanaye na jam’iyyunsu.
Jam’iyyun sun yi wannan roko ne a ranar Talata yayin taron tuntubar juna karo na biyu da hukamar INEC ta shirya ya gudana tare da jam’iyyun siyasa a birnin Abuja.
A watan Fabrairu ne dai Hukumar Zaben (INEC) ta sake duba jadawalin zaben shekarar 2023 bayan da Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar zabe ta 2022.
Dangane da sabuwar dokar, hukumar ta ware ranar 4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yunin shekarar 2022 domin gudanar da zabukan fitar da gwananye na jam’iyyu.
A makon da ya gabata ne hukumar ta kara tabbatar da cewa wa’adin gudanar da zaben fidda gwani yana nan daram bai Chanja ba.
Da yake martani kan bukatar da gamayyar jamiyyun suka shigar, shugaban hukumar ta INEC Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ba za ta sake kara wa’adin da aka bayar a baya ba domin hakan zai haifar da yamutsi.
“A nan ina kara jaddada matsayar hukumar Zabe na cewa ba za a sake duba jadawalin zaben shekara mai zuwa ta 2023 ba.













































