Farashin Litar Man Fetur Ya Kara Tashi Zuwa N617 a Najeriya 

Fuel pump
Fuel pump

Rahoton Daily Trust da safiyar Talata, ya tabbatar da cewa farashin litar man fetur a Najeriya ya ƙara tashi zuwa N617 a tsakiyar birnin tarayya Abuja. Yayin wata ziyara da wakilin jaridar ya kai gidan mai mallakin kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da ke Abuja ya tabbatar da cewa farashin ya tashi daga N539 zuwa N617 kan kowace lita.

Wani kwastoma na daban wanda ya ƙara tabbatar da wannan ci gaban ga wakilin jaridar Daily Trust, ya shaida cewa, “Tabbas da gaske ne, yanzu na sayi mai kan N617 kowace lita.” A halin yanzu ba bu wanda ya san dalilin tashin farashi litar mai ba zato ba tsammani kuma mahukunta ba su ce komai dangane da lamarin ba har kawo yanzu.

Sai dai ana hasashen cewa tsadar man ba zai rasa nasaba da hasashen da ‘yan kasuwar mai suka yi a kwanakin baya cewa Litar mai ka iya kai wa N700 nan gaba. Hukumar kula da harkokin Man Fetur ta Najeriya (NDMPRA) ba ta ce komai ba kan sakon da jaridar ta aike mata don tabbatarwa har zuwa yanzu da muke haɗa muku rahoto.

Karin bayani na nan tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here