Gwamnatin jihar Abia ta gano ma’aikatan bogi 2300, inda ta samu nasarar dakatar da zirarewar miliyan 220

Alex Otti Abia LP Candidate 1 750x430
Alex Otti Abia LP Candidate 1 750x430

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ce ya sami damar dakatar da zirarewar Naira miliyan 220 a tsarin biyan albashi.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan, Kazie Uko ya fitar ranar Litinin a Umuahia

Sanarwa ta ce an samu damar dakatar da zirarewar kudin ne sakamakon sabon tsarin tan-tan ce ma’aikata da gwamnati jihar ta ballo dashi domin gano ma’aikatan bogi.

Sanarwar ta kara da cewa sakamakon tsarin tan tan cewar, gwamnatin tayi nasarar gano ma’aikatan boge 2,300 da ake biya albashi duk wata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here