Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya fice daga APC zuwa ADC, tana bayyana zargin a matsayin ƙarya kuma abin yaudara.
A cewar sanarwar da Hassan Abubakar, sakataren shirya harkokin jam’iyyar na jihar kuma mai kula da sabon tsarin rajistar mambobinta, ya fitar, ya ce rahotannin ba su da tushe kuma an ƙirƙire su ne domin ruɗar jama’a da haddasa rikici a cikin APC.
Jam’iyyar ta jaddada cewa Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, har yanzu cikakken ɗan APC ne mai katin zama mamba, kuma bai taɓa ficewa ko tunanin ficewa daga jam’iyyar ba.
Sanarwar ta bayyana cewa hoton da ake yaɗawa a matsayin hujjar sauya sheƙar an ɗauke shi ne a yayin sabon shirin rajistar mambobi da sabunta bayanan mambobin APC da ke gudana a faɗin ƙasar, wanda aka tsara domin ƙarfafa bayanan jam’iyyar da dimokuraɗiyyar cikin gida.
Jam’iyyar ta ce hoton ya nuna Sanata Adamu ne yana sabunta rijistar da ta zama memba na APC bisa tanade-tanaden kundin tsarin jam’iyyar da kuma shirin gyare-gyaren ta, ba wai wata alamar sauya sheƙa ba.
APC ta soki ƙoƙarin wasu da ba a bayyana sunayensu ba na karkatar da sahihin aikin jam’iyya zuwa labarin ƙarya, tana mai cewa biyayyar Sanata Adamu da gudummawarsa ga bunƙasa da daidaiton APC a rubuce suke kuma ba abin musantawa ba ne.
Jam’iyyar, ta yi kira ga mambobi, kafafen watsa labarai da jama’a da su yi watsi da jita-jitar, su dogara da sahihan bayanai daga tushe masu inganci.
NAN













































