Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Dattijai Makon Nan

Senate
Senate

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tura sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa a makon nan matuƙar ba a samu sauyi da ka iya kawo cikas ba. Wasu majiyoyi masu ƙarfi daga fadar shugaban ƙasa sun nuna cewa tun da jima wa Tinubu ya gama tsara ministocinsa amma an samu wasu ‘yan sauye-sauye daga baya.

Wata majiya a fadar shugaban ƙasa, wacce ta nemi a sakaya bayanantaa, ta shaida cewa: “Tun tuni da daɗe wa aka gama rubuta sunayen Ministoci amma daga baya shugaban ƙasa ya yi wasu sauye-sauye a wasu jihohi.”

“Muna tsammanin za a tura sunayen ministocin ga majalisar tarayya tsakanin ranar Laraba da Alhamis matuƙar ba a samu wani ci gaba da ka iya kawo ƙarin jinkiri ba.”

“Ana tsammanin shugaban ƙasa ya naɗa mukarrabansa kafin ranar 26 ga watan Yuli, 2023 kuma ina da tabbacin za a tura sunayen ga majalisar dattawa a makon nan.”

Idan baku manta ba a kwanakin bayan an yaɗa wasu sunaye da ake tsammanin sune Ministoci yayin da shugaban ƙasa ya bar yan Najeriya suna kintace kan waɗanda zai naɗa.

A halin yanzu ana dakon jiran a gani ko Tinubu zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa kamar yadda ake hasashe a wasu sassan ƙasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here