Gwamnan Bauchi Ya Rushe Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomin Jihar 

Bala Mohammed new 2
Bala Mohammed new 2

Gwamnan Bala Abdulkadir Mohammed, ya sanar da rushe dukkanin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan ya ce an dauki matakin na rushe shugabannin ne sakamakon karewa da wa’adin mulkinsu ya yi.

Sanarwar ta fito ne ranar Talata 18 ga watan Yuli, ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammad Kashim, wacce ya rabawa manema labarai a Bauchi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an umarci shugabannin da aka sauke da su mika ragamar mulki ga shugabannin gudanarwa na kananan hukumominsu.

Ta kara da cewa shugabannin gudanarwar ne za su ci gaba da rike kananan hukumomin har zuwa lokacin da za a nada sababbin shugabannin riko. Bala Mohammed ya kuma yi wa daukacin shugabannin na riko da aka sauke fatan samun nasara a ayyukansu na gaba tare da gode musu bisa gudummar da suka bai wa jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here