Sabowar Shekarar Musulunci: Gwamnatin Kano ta bada hutun kwana daya

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin kano ta ayyana ranar Talata 19 ga wannan watan a matsayin ranar hutun sabowar shekarar musulinci, hira ta 1445.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye ya fitar a madadin gwamnan jihar Abba Kabir Yusif.

Gwamnan ya kuma taya musulmaman duniya murnanr zagayowar shekarar, inda kuma ya nemi da al’umma su dage wajan addu’ar zaman lafiya da arziki ma durewa a jihar da kuma kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here