Mai girma Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin wasu mukami a jihar Kano kamar yadda wata sanarwa ta fito a safiyar Larabar nan. Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda shi ne babban Sakataren yada labarai na Gwamnan Kano ya fitar da jawabi a shafinsa na Facebook dazu.
Abba Gida Gida ya nada sababbin shugabannin hukumomin gwamnati da su ka hada da RUWASA, KASCO da kuma hukumar tace fina-finai.
Daga cikin wadanda aka ba mukaman akwai Sani Bala, Dahir M. Hashim da Tukur Bala Sagagi.
Jerin mukaman da aka bada
1. Injiniya Ado Ibrahim Umar, Shugaban kamfanin wutar lantarki (KHEDCO).
2. Alhaji Auwalu Mukhtar Bichi, Shugaban kamfanin jawo hannun jari (KSIP).
3. Dr. Farouq Kurawa, Shugaban hukumar kula da aikin gona da raya karkara (KNARDA)
4. Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Shugaban hukumar samar da kayan gona (KASCO)
5. Hon. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Shugaban aikin SKP
6. Hon. Sadiq Kura Muhammad, Shugaban gidan dabbobi (ZGK)
7. Injiniya Sani Bala, Shugaban hukumar kula da wutar lantarki a karkara (REB)
8. Hon. Shamwilu Gezawa, Shugaban hukumar ruwa (RUWASA)
9. Alh. Tukur Bala Sagagi, Shugaban hukumar yawon bude ido
10. Alh. Yahaya Muhammad, Shugaban kamfanin madaba’ar Kano.
11. Hon. Adamu Yahaya, Mataimakin shugaban kamfanin madaba’ar Kano.
12. Abba El-mustapha, Shugaban hukumar tace fina-finai.
13. Dr. Muhammad S. Khalil, Shugaban hukumar kula da zaizayewar kasa da sauyin yanayi (KN-WECCMA)
14. Dr. Dahir M. Hashim, Mai kula da hukumar kula da zaizayewar kasa da sauyin yanayi (KN-WECCMA)