Gwamnatin jihar Kano ta shirya gudanar da auren gata ga ma’aurata 1,500 – Hukuma

FB IMG 1773953278977

Gwamnatin jihar Kano, ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da auren gata ga ma’aurata dubu daya da dari biyar a karkashin shirin gwamnatin na Auren Gata.

Mataimakin babban kwamandan Hisba na jihar Kano, Dr Mujahideen Aminudeen ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Alhamis a Kano.

Aminudeen, ya ce shirin auren gatan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kaddamar na cikin kokarin da gwamnatin take na karfafa gwiwar masu karamin karfi a jihar.

Ya kuma bayyana cewa an dauki matakin sake yin auren gatan ne bayan nasarar da aka samu a shirin da aka yi a baya.

A cewarsa samu kyakykyawan sakamakon da aka yi a shirin auren gata na farko ne ya karfafa gwiwar gwamnati har yasa ta dauki wannan mataki na sake yin aure domin kara karfafa shirin.

Aminudeen ya kuma ce gwamna ya bada umarnin a kammala duk wani shirye-shirye zuwa karshen wata mai kamawa na Mayu

Ya kuma jaddada cewa wajibi ne ma’auratan su cika duk wasu sharuda da shirin ya tsara kafin shiga tsairin na auren gata.

“Dole a samu amincewa daga shugabannin gargajiya na yankin da ma’auratan suka fito, sai kuma sun kuma sun tabbatar wa hukumar Hisba cewa za su kasance a matsayin mata da miji kafin su cike takardar da za a basu.” Inji shi.

Haka zalika, Aminudeen ya karyata rade-radin da ake na cewa hukumar na tursasawa masu dole sai sun yi aure, ba kuma a yin adalci a lokacin gudanar da shi “babu wanda ake tilastawa, ma’aurata na yin aure ne bisa soyayya da kauna.”

Aminudeen ya kuma kara da cewa, yin gwajin lafiya ga ma’auratan wajibi ne don tabbatar da lafiyarsu, inda ya bayyana gwaje-gwajen da suka hada da HIV da na jini da kuma na lafiya jiki baki daya.

Ya kuma cewa gwajin ciki wajibi ne ga matan da za a aurar domin kare martaba da kimar ma’auratan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here