Iyalan dalibin Jami’ar Jos, John Arum Azi da aka yi garkuwa da shi, sun tabbatar da cewa an sake shi. Sakin dalibin ya biyo bayan biyan kudin fansa na naira miliyan 6 da ‘yan uwan dalibin suka yi bayan kwanaki 10 a hannun masu garkuwar.
Azi, dalibi a sashin koyar da ilimin kananan yara, ya taso ne daga Jos a jihar Plateau zuwa Zariya a jihar Kaduna lokacin da masu garkuwa da mutanan suka yi garkuwa da shi.
Bayan fitar wani bidiyo a shafukan sada zumunta, da ya nuna yadda masu garkuwa da dalibin ke azaftar da shi, wanda suka nemi kudin fansa na Naira miliyan 30 ko kuma su kashe shi, ya ja hankalin jama’a a kafafen.
Jaridar Vanguard tace, bayan tattaunawa tsakanin ‘yan uwan dalibin da masu garkuwar, sun cimma matsayar biyan Naira miliyan 6 da jama’a suka hada a fadin Nijeriya.
Duk da biyan wannan kudin, masu garkuwar sun kuma sake neman karin Naira miliyan 4.
An tabbatar da sakin dalibin a ranar Laraba a wani bidiyo da ‘yan uwan dalibin suka dura a shafin sada zumunta.











































