Shida daga cikin mambobin majalisar wakilai ta kasa, sun sauya shiga daga jam’iyyun NNPP da PDP tare da komawa jam’iyyun APC da ADC.
Yayin da yake karanta wasikun sauya shekar mambobin a zaman da majalisar ta yi a ranar Laraba, shugaban majalisar Abbas Tajudeen ya ce hudu daga cikin ‘yan majalisun, wadanda suka fito daga Kano sun sauya sheka daga NNPP zuwa ADC.
Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo, Adamu Wakili ne ya fara sanar da sauya shekar ta sa, yayin da daga bisani Umar Zakari da Umar Datti da kuma Abdulhakeem Ado suma suka sanar da sauya shekar ta su zuwa jam’iyyar ADC daga NNPP.
‘Yan majalisar sun bayyana rikice-rikicen cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP a matsayin dalilin sauya shekar ta su.
Daga jihar Zamfara, dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gusau da Tsafe, Ahmadu Kabiru ya sanar da barin jam’iyyar PDP, inda ya bayyana shiga jam’iyyar APC, inda ya ce a shirye yake ya taimaki shugaban kasa Bola Tinubu a shirinsa na Renewed Hope Agenda.
Shima a nasa bangaren, dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Ahiazu da Ezinihitte Mbaise daga jihar Imo, Chinedu Martins ya sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki.
Dan majalisa y ace dama ya dade da komawa APC a can mazabarsa tun a watan Maris da ya gabata.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yace, da wannan sauya shekar da mambobin suka yi, jam’iyya mai mulki ta APC ta kara zama mafi rinjayi a zauran majalisar da mambobi 282, yayin da jam’iyyar PDP ke da 30.
ADC na da mambobi 24, yayin da LP da Accord Party da APGA da APP da SDP da kuma NNPP ke da mambobi 24 a zauran majalisar ta wakilai.












































