Gwamnatin jihar Kano ta tuhumi tsohon babban jami’i kuma manajan darakta na kamfanin samar da noma na jihar, (KASCO), Bala Muhammad Inuwa, dansa da wasu mutane biyu kan laifin zamba sama da naira biliyan hudu.
Ofishin babban lauyan jihar Kano, kuma kwamishinan shari’a ne ya shigar da karar da ake tuhumarsu, biyo bayan binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ke yi.
Hukumar ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa wadanda ake tuhumar sun karkatar da sama da Naira biliyan 4 daga asusun kamfanin samar da noma na jihar zuwa asusun sirri.
An fara gabatar da karar ne a kotu a ranar 6 ga watan Agusta, 2023 An kuma mika ta ga wani alkalin babbar kotun jihar Kano, Hafsat Sani.