Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi kakkausar suka ga ofishin jakadancin kasar Canada kan hana shugaban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa biza.
Janar Musa ya bayyana a ranar Alhamis, yayin taron lacca na shekara-shekara na kungiyar Cibiyar Nazarin tsaro ta kasa, cewa an hana shi da wasu ‘yan tawagarsa takardar izinin halartar wani taron karrama mayaka da aka yi a kasar Canada.
Tunji-Ojo da yake magana a gidan Talabijin na Channels cikin shirin Sunrise Daily a ranar Juma’a, ya yi Allah-wadai da matakin na ofishin jakadancin, yana mai cewa rashin mutunta Najeriya a matsayin kasa daya ne, har ma ya ce, yaya talakawan Najeriya za su yi kenan idan har babban hafsan sojin kasar zai fuskanci irin wannan yanayi.
Karin karatu; UAE Ta Soke Haramcin Bai Wa ’Yan Najeriya Biza
Ministan ya bayyana matukar wahala wajen tabbatar da matakin na Canada, yana mai jaddada cewa duk wata damuwa da ofishin jakadancin ya yi da an magance ta ta hanyoyin diflomasiyya. Ya kuma ba da tabbacin cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar za ta dauki matakan da suka dace don warware matsalar tare da tabbatar da mutunta juna a tsakanin kasashen biyu.
A halin da ake ciki, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, tun farko ya yi Allah wadai da abin da kasar Canada ta yi, inda ya bayyana takaicinsa a dai wannan taron da Janar Musa ya bayyana.