Wa ake sa rai zai maye gurbin Pochettino?

images 1
images 1

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain na shirin raba gari da mai horar da ‘Yan wasanta Mauricio Pochettino dan kasar Argentina.

PSG dai ta zama zakara a gasar Ligue 1 ta kakar wasannin shekarar 2021/2022 bayan tashi wasa 1-1 da takwararta ta Lens a ranar Asabar.

Lamarin da ya sanya shugabancin kungiyar fara daukar matakin kwaskawarima sakamakon ficewa daga gasar kofin turai a zagaye na 16 da tawagar ta yi.

Rahotanni a baya dai sun bayyana cewa tsohon mai horar da Tottenham da shi ne zai kasance a filin wasa na Old Trafford, sai dai kungiyar tuni ta dauki matakin amincewa da nadin Erik ten Hag a matsayin wanda zai jagoranci United a kakar wasanni mai zuwa.

Wannan lamari dai ya sanya PSG daukar matakin raba gari da dan kasar Argentina wanda ake gani kungiyar na shirin sallamar ‘yan wasa da dama domin sake zubi na tunkarar kakar wasanni mai zuwa.

Sakamakon yadda tawagar ke da ‘yan wasa irinsu Lionel Messi da Neymar JR da kuma Kliyn Mbappe amma ta gaza yin abin a zo a gani a gasar cin kofin zakarun turai ta kakar wasannin shekarar 2021/2022

Tuni dai aka fara hasashen cewa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Antonio Conte, ne zai maye gurbin Moricious Pochettino da zarar kungiyar PSG ta fitar da sanarwar sallamarsa.

Pochettino dai yanzu haka na jagorantar Spurs da take a mataki na shida a gasar Frimiya wanda maki biyu ne tsakaninta da Arsenal da kawo yanzu wasanni biyar ne suka rage a kammala kakar wasanni ta bana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here