Zaben 2023: Kwamishina a Jihar Borno ya bar aiki domin tsayawa takara

babagana umara zulum 1
babagana umara zulum 1

Kwamishinan Ma’aikatar jin kai da rage radadin talauci ta jihar Borno Mista Nuhu Clark, ya ajiye mukaminsa domin tsayawa takarar kujerar Majalisar dokokin jiha mai wakiltar Karamar hukumar Chibok a Jam’iyyar APC.

A zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ranar Litinin a MaiDuguri Clark, ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar ne domin tabbatar da wakilcin al’ummar Chibok cikin nagarta.

Clark wanda ya taba zama shugaban karamar Hukumar ta Chibok a 1999 yace har yanzu yana tare da al’ummarsa, kuma ayyukan ma da ya gudanar a wancan lokaci al’umma suna sane basu manta dasu ba.

Ya kuma godewa Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum bisa damar da ya bashi ya yi aiki a matsayin Kwamishina.

Kamfanin dillancin Labarai NAN ya rawaito cewa Kwamishinan Ma’aikatar noma Bukar Talba shima tuni ya ajiye aikinsa.

Talba dai na neman tsayawa takarar Dan Majalisar wakilan Tarayya mai wakiltar mazabun Nganzai/Monguno da kuma Marte a zauren Majalisar Tarayya, karkashin inuwar Jam’iyyar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here