An Harbe Mutum Takwas Kusa Da Barikin Soja A Taraba

1688331157283
1688331157283

Mahara sun harbe mutune takwas har lahira a kusa da ƙofar shiga barikin sojoji dake Takum a jihar Taraba.

Mazauna garin Takum sun shaidawa wakilin Aminiya cewa an yi kisan ne da yammacin Talata.

Wani shaida da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce waɗanda aka harbe na kan hanyarsu ne ta dawowa daga coci a wani ƙauye da ke kusa da barkin sojin.

Ya ce an harbe su ne daf da ƙofar shiga barikin.

Sai dai, kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Taraba, SP Usman Abdullahi da mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar soji Lt. Oni sun ce ba su samu labarin afkuwar lamarin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here