Hubby Gwamnatin jihar Kwara ta sake dawo da yin amfani da hijabi ga dalibai ’yan mata musulmi da suke da sha’awar sanya hijabi a makarantun gwamnatin jihar.
Kwamishiniyar ilimi da ci gaban al’umma ta jihar, Sa’adatu Madibbo-Kawu, ce ta bayyana hakan a yayin wani taron tattaunawa da aka yi tsakanin masu ruwa da tsaki na musulmi da kirista a garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun, wanda aka gudanar a hedikwatar ma’aikatar dake Ilorin a ranar Litinin din da ta gabata.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai na ma’aikatar ilimi da ci gaban al’umma Yakub Aliagan ya rabawa manema labarai a ranar Talata ta tabbatar da faruwar lamarin.
“Rikicin Hijabi: Gwamnatin Kwara ta ba da umarnin bude makarantu 10 cikin gaggawa Ya ci gaba da cewa, “Bayanin manufofin gwamnatin jihar Kwara na barin ‘yan mata musulmai masu son sanya hijabi a duk makarantun gwamnati, ciki har da wadanda ake ba da tallafi, ya zama dole.
“Wannan ya yi daidai da hukunce-hukuncen kotunan shari’a da kuma kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce saboda haka, ana kira ga shugabannin Musulmi da Kirista da su bada hadin kai domin samun zaman lafiya a jihar.
‘’ Bayan haka Sa’adatu Modibbo-Kawu ta umurci shugabannin makarantar sakandaren Baptist ta Oyun, Ijagbo da su gaggauta aiwatar da sanarwar manufofin amfani da hijabi da aka amince da su a makarantun gwamnati.
‘’Kwamishinan ta yi gargadin cewa duk wanda ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar Kwara zai fuskanci fushin doka.













































