Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) dake jihar Katsina, tace ta samu sahalewar fara bada sabbin darisa 23 a matakin digiri na farko da kuma 21 a matakin PG.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Jami’ar, Malam Habib Umar-Amin ya rabawa manema labarai ranar Laraba a Katsina.
Read also: Gobara ta tashi a gidan Ganduje dake Kano
Ya ce sabbin darisan da hukumar dake kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta amince da su, za’a fara bada su a zangon karatu na 2023/2024.
Read also: HOTUNA: Gobara ta cinye kasuwar kayan gida, daki da ofis a Kano
Sabbin darisan sune B.Sc Mass Communication, LL.B Law, B.Eng, Mechatronics Engineering, and B.Sc International Relations da kuma Diplomacy.
Read also: ASUU za ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya
Sauran sune B.URP Urban and Regional Planning, B.Sc Applied Geophysics, B.Tech Entrepreneurship, B.Tech Textile Design Technology da sauran su.













































