Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta dakatar da daya daga cikin ma’aikatanta saboda karbar kudi ba bisa ka’ida ba daga daliban da ba su ji ba su gani ba.
An bayyana dakatarwar ne a cikin sanarwar hukumar a ranar Litinin, yayin da JAMB ta sake jaddada aniyarta na tsaftace hanyoyin shiga makarantu da jarabawa.
Read also: Barau ya yabawa Tinubu kan sauya sunan Jami’ar Ilimi ta tarayya Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule
Hukumar ta ce matakin da aka dauka kan ma’aikacin da ba a bayyana sunansa ba ya nuna cewa kokarinta na kawar da damfara a tsarin ba wai ga ‘yan damfara daga waje kadai ya tsaya ba.
“Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta dakatar da daya daga cikin ma’aikatanta saboda karbar kudi ba bisa ka’ida ba daga daliban da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani kudirinta na fitar da bata gari daga tsarin.
“Saboda haka, Hukumar ta sake gargadin dukkan ma’aikata da su guji duk wani hali mara kyau, musamman ayyukan da za su iya zubar da mutuncin Hukumar ko cin zarafin dalibai da jama’a, domin irin wadannan ayyuka za su jawo sakamako mai tsanani bisa ga ka’idojin da aka gindaya,” in ji JAMB.
Read also: Kotu ta umarci wata Jami’a ta dawo da malamin da ta kora
Hukumar ta jaddada cewa irin kudirin da Take da shi na hukunta masu damfara daga wajen hukumar shi ake amfani da shi wajen magance laifin a ciki gida.
“Hukumar ta bayyana cewa kudirinta na tsaftace hanyoyin shiga makarantu da jarabawa ba wai ga masu damfara na waje kadai take mayar da hankali ba, ta jaddada cewa irin kudirin da take da shi ba tare da gajiyawa ba na hukunta masu damfara a wajen Hukumar shi ake amfani da shi wajen magance badakala ta ciki gida.”
JAMB ta ce korar kamar wani gargadi ne karara ga ma’aikatanta cewa manufofinta na babu sani babu sabo kan cin hanci da rashawa da badakala na shafar dukkan ma’aikata, ba tare da la’akari da mukamansu ba.
Hukumar ta yi gargadi cewa ma’aikatan da aka samu suna aikata dabi’un da za su iya kawo cikas ga ayyukanta za su fuskanci hukunci bisa ga ka’idojin da aka gindaya.
Read also: Shugaba Tinubu ya sake gabatar da shirin ciyar da Yara makaranta
Ta sake tabbatar da kudirinta na kiyaye abin da ta bayyana a matsayin ma’aikata masu tsafta, rikon amana da kwarewa.













































