Kotu ta umarci wata Jami’a ta dawo da malamin da ta kora

Court Gavel
Court Gavel

Kotun masana’antu ta kasa ta umarci Jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama da ke Yola da ta mayar da wani malami Dakta Sa’idu Adamu bakin aiki.

Kotun ta kuma bayar da umarnin mayar da Adamu kan mukaminsa na Malami na daya tare da biyansa albashi da alawus-alawus da sauran hakkokinsa.

Bugu da kari, kotun ta ba da umarnin a ƙidaya kudin da ya kamata a bashi tun daga Yuli, 2015, wanda shine lokacin da aka kore sa ba bisa ka’ida ba.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Sanusi Kado ya ce mai karar bai taba zuwa gaban wani kwamitin ladabtarwa ba.

Alkalin ya ci gaba da cewa, ba a ba wa mai karar damar yin bayani da zargin da aka yi masa na dakatar da aikinsa ba.

Ya kuma kara da cewa amincewar majalisar gudanarwar ta dogara ne akan takardar da shugaban Jami’ar ya bayar, ba rahoton kwamitin ladabtarwa wanda ba a taba gabatar da shi a gaban kwamitin ba.

Alkalin ya ce wannan dabi’a ya saba wa tsarin da aka tsara na ladabtar da ma’aikatan jami’ar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here