An nada wa Jami’ar Sule Lamido ta Jihar Jigawa sabon shugaba

Sule Lamido University SLU 750x430
Sule Lamido University SLU 750x430

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya amince da nadin Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai a matsayin sabon shugaban jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar aka rabawa manema labarai a Dutse.

Ibrahim ya ce nadin sabon shugaban ya biyo bayan shawarwarin da majalisar gudanarwar jami’ar ta bayar kamar yadda dokar da ta kafa ta ta tanada.

“Har zuwa nadinsa Farfesa Yakasai shi ne shugaban kwamitin tabbatar da ingancin ayyuka na sassa a Jami’ar Bayero dake Kano.

“Sabon shugaban wanda ke da digirin digirgir a fannin halayyar Dan Adam, yana da kwarewa a fannin koyarwa a matakai daban-daban.

Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

Sakataren gwamnatin jihar ya kara da cewa sabon shugaban ya yi aiki a matsayin Shugaban Sashe, Mataimakin shugaban tsangaya da kuma shugaban tsangaya.

“Sabon shugaban jami’ar ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero a fannin ilimi da tarihi a shekarar 1986.

Sannan ya samu digirin na biyu a fannin Ilimin Halayyar Dan Adam a shekarar 1991.

Daga nan ne kuma ya koma jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi digirin digirgir a fannin Ilimin Halayyar Dan Adam a 2000.

“Ya fara aiki a Jami’ar Bayero dake Kano tun a shekarar 1991, ya kuma zama babban malami kafin a nada shi shugaban kwamitin tabbatar da ingancin ayyuka na sassan Jami’ar Bayero a shekarar 2021.

“Shi Farfesa ne a fannin ilimin halayyar Dan Adam kuma mamba a cibiyar Ilimi da Shawarwari ta kasa.”

A cewar sakataren gwamnatin, nadin ya fara aiki ne tun daga ranar 5 ga watan Disambar shekarar da muke ciki ta 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here