An saki Emefiele daga gidan yarin Kuje bayan cika sharuddan beli

Emefiele, kotu, tsare, EFCC, zargin, almundahana, zamba
Mai shari’a Rahman Oshodi na kotun hukunta manyan laifuka na musamman a Ikeja a ranar Litinin din da ta gabata ya tasa keyar tsohon gwamnan CBN Mista Godwin...
Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele ya cika sharuddan belin da mai shari’a Hamza Mu’auz na babbar kotun tarayya ya bayar.

Mai shari’a Mu’auz ya bayar da belin Emefiele, ne a kan kudi Naira miliyan 300.

An kuma bukaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda suke da kadarori a Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja.

Yanzu haka dai Godwin Emefiele, ya koma gida bayan ya cika sharuddan belin da kotu ta bayar.

Mai magana da yawun Gidan Yari na Kuje da ke Abuja, shi ne ya tabbatar da sakin tsohon gwamnan babban bannmkin da yammacin ranar Juma’a.

Karanta wannan: An nada wa Jami’ar Sule Lamido ta Jihar Jigawa sabon shugaba

Tun a ranar 22 ga watan Nuwamba ne Babbar Kotun ta ba da belinsa kan naira miliyan 300 tare da gabatar da mutum biyu da ke da kadarori a Maitama da ke Abuja.

Godwin Emefiele 750x430

Kazalika, kotun ta umarce shi da ya mika mata dukkan takardunsa na tafiye-tafiye.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani rahoto da mai bincke na musamman, Jim Obazee, ya zarge shi da karya dokar kwangila da sayen kayayyakin gwamnati.

Rahoton Obazee, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuli don ya binciki CBN a karkashin mulkin Emefiele, ya zarge shi da amfani da wakilansa wajen sayen Bankin Union, da kuma yin amfani da karfin ikonsa a cinikin bankunan Polaris da Keystone.

Gwamnatin Tinubu na zargin tsohon gwamnan babban bankin da aikata almundahanar kudi naira biliyan 1 da miliyan 200, zargin da ya musanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here