Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar arewa maso yamma Operation HADARIN DAJI, a ranar Juma’a, sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta saka a shafin ta na X ranar Asabar.
Sanarwar ta ce “An sami nasarar ceto su ne a ranar 22 ga Disamba, 2023, lokacin da sojoji suka fatattaki ‘yan ta’addan a kauyukan Saruwa, Kubuta, Gundumi da dajin Bunwanga Gundumi a karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato.
“A yayin farmakin, sojojin na OPHD sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe ‘yan ta’adda da dama.”
“Wadanda aka ceto sun hada da maza 14, mata 32, da kuma yara shida wadanda za a duba lafiyarsu, za a kuma mika su ga hukumomin da suka dace domin hada su da iyalansu.”