Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da rundunar Operation Hadarin Daji, sun ce sun kashe ‘yan bindiga a kauyen Yar Tashar na Karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotonni sun ce an kashen ‘yan bindigar ne a lokacin da suke girbe kayan amfanin gona da suka shuka a gonakinsu da ke kauyen.
Daraktan yada labarai na na hukumar tsaron kasar Manjo janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin da safe.
Ya ce a lokacin harin dakarun sojin sun kwato babur daya, tare da makamai da wasu kayayyaki daga wajen ‘yan bindigar.
Jami’in sojin ya kuma ce dakarun kasar sun samu nasarar dakile wani harin ‘yan bindigar a kauyen Gamraki na gundumar Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu a jihar.