Malamai 3 ne kacal a Makarantar Sakandiren yaran mu Mata- Iyaye a Sumaila

ladies 750x430
ladies 750x430
Iyaye a mazabar Sitti da ke karamar hukumar Sumaila a jihar Kano sun koka kan rashin isassun malamai a makarantar sakandiren mata ta gwamnati dake yankin.

Iyayen sun koka da halin da ake ciki ne yayin taron da wata kungiya mai zaman kanta mai suna “PAGED Initiative” ta shirya a makarantar sakandiren yankin.

Dagacin garin Sitti, Ado Auwal Sale ya ce ilimin ‘ya’ya mata yana da muhimmanci amma rashin isassun malamai da ajujuwa da kayan koyarwa na hana su samun ilimi mai inganci.

Basheer Sayyadi Kabir, shi ne shugaban kungiyar ci gaban Sitti, yace rashin isassun malamai da ajujuwa ya kasance babbar matsalar ilimi a yankin.

Don haka ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta dauki karin malamai a makarantun sakandiren mata na Sumaila domin bunkasa harkar ilimi a yankin.

ladies 750x430, Makarantar

Kazalika, mataimakin shugaban kungiyar Malaman sa kai na Sitti Sani Garba Yelwa ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru tara yana aikin sa kai a makarantar.

Wani mazaunin garin Sitti, Shuaibu Sale ya ce rashin samar da dakin gwaje-gwaje na kimiyya a makarantar sakandiren mata ta Sitti ya zama wani kalubale ga al’umma.

Karanta wannan: Sojoji sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su a Sokoto

Jami’ar da ke kula da shirin AGILE a karamar hukumar Sumaila, Hafsat Ado Hamza ta ce iyaye a yankin ba sa maraba da ilimin yara mata.

Don haka ta bukaci gwamnati da kungiyoyi masu zaman kan su, su shirya gangamin wayar da kan iyaye a matsayin wani kokari na karfafa ilimin yara mata a yankin.

A nata bangaren, Daraktar shirin PAGED, Ummi Bukar ta ce ya kamata a bai wa ilimin yara mata fifiko domin yana daga cikin muhimman hakkokin bil’adama.

Bukar ta ce, PAGED Initiative ta shirya taron ne don wayar da kan al’umma a wani bangare na kokarin tallafawa da inganta ilimin ‘ya’ya mata.

Tace irin wannan taro na da nufin dakile tarnakin da ya dabaibaye harkokin ilimin ‘ya’ya mata da kuma bunkasa kwazon su a cikin al’umma.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa PAGED Initiative ta gabatar da wani takaitaccen shiri na koyar da yara mata domin zaburar da su, da nufin bunkasa ilimin yara mata a Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here