Gwamnatin Kaduna za ta gina makarantu 359 da ‘yan ta’adda suka mamaye

'Yan Ta'adda, gwamnan, kaduna, jihar, gida, makarantu
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya koka da raguwar karatun dalibai a makarantu a fadin jihar. Sani, wanda ya nuna damuwarsa kan wannan ci gaban, ya...

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya koka da raguwar karatun dalibai a makarantu a fadin jihar.

Sani, wanda ya nuna damuwarsa kan wannan ci gaban, ya danganta lamarin da yawaitar tabarbarewar tsaro, da ake samu ta hanyar yin garkuwa da mutane da sauran laifuffukan da ke faruwa a jihar.

Ya bayyana cewa gwamnati ta fara wani yunkuri na mayar da makarantu 359 daga yankunan da ‘yan ta’adda suka mamaye tare da hade su da sauran makarantu a wurare masu aminci.

Karin labari: Kotu ta bada belin Hadi Sirika da ‘yarsa da wasu mutum 2 kan kudi miliyan 100 ga kowannensu

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake bayyana bude wani shiri na kwana daya wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shirya a Kaduna a ranar Laraba.

Sani ya bayyana a matsayin wanda ya dace da taken shirin ‘Karfafa Juriyar Tsaro da Hadin Kan Al’umomin Da ke Wajen Kare Ilimi’.

“Abubuwan da suka faru kamar satar dalibai 135 daga makarantar firamare da karamar sakandare ta LEA da Kuriga da karamar hukumar Chikun, sun nuna mummunan tasirin rashin tsaro ga samun ilimi da tsaro.

Karin labari: Ambaliya: Gwamna Namadi ya bada umarnin gina katangar ruwa a Jigawa

“Domin tabbatar da cewa ba a katse karatun yaranmu a yankunan da ake fama da rikici da ‘yan ta’adda ba, mun fara hade makarantu 359 da wadanda ke wurare masu aminci,” inji gwamnan.

Sani ya koka da abin da ya bayyana a matsayin raguwar yawan daliban makarantu a jihar sakamakon rashin tsaro.

Ya ci gaba da cewa, “Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke yaki da ‘yan fashi da ta’addanci da garkuwa da mutane da sauran laifuka.”

Karin labari: An kama mutum 17 da zargin hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Gwamnan ya yabawa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Olukayode Egbetokun bisa kafa kungiyar kare makarantu na wani shiri mai himma da nufin inganta tsaro da tsaro a cibiyoyin ilimi a fadin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here