Majalisar wakilan Najeriya ta zartar da kudurin binciken kwangilar titin Legas zuwa Calabar

Majalisar, Wakilan, Najeriya, bunciken, kwangila, legas, calabar, kudurin, titin
Majalisar Wakilai ta zartar da wani kuduri na binciken tsarin sayan kayayyaki wajen bayar da kwangilar titin Legas zuwa Kalaba da ya kai tiriliyan 15...

Majalisar Wakilai ta zartar da wani kuduri na binciken tsarin sayan kayayyaki wajen bayar da kwangilar titin Legas zuwa Kalaba da ya kai tiriliyan 15.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na muhimmancin kasa da Austine Achado ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.

Majalisar ta ce an keta dokar sayo kayayyaki ta shekarar 2007, kuma ba a ba da wasu amincewar da majalisar ta yi ba kamar yadda doka ta tanada.

Karin labari: Gwamnatin Kaduna za ta gina makarantu 359 da ‘yan ta’adda suka mamaye

Kwanan nan Ministan Ayyuka Dave Umahi ya ce aikin titin bakin tekun Legas zuwa Calabar, zai ci Naira biliyan 4 a kowace kilomita.

Za’a gina titin bakin teku mai tsawon kilomita 700 daga Legas zuwa Calabar a kan Naira tiriliyan 15, kuma kilomita daya daga cikin titin zai ci Naira biliyan hudu.

Karin labari: ASUU ta koka kan watsi da wasu bukatun Jami’ar Yusuf Maitama a Kano

An yi ne don a hada hanya da Legas zuwa Kuros Riba zuwa jihohin Ogun da Ondo da Delta da Bayelsa da Ribas da kuma Akwa Ibom kafin ta kai ga Cross River.

Aikin dai ya sha suka sosai daga ‘yan Najeriya da dama ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (LP) a zaben 2023, Peter Obi, wanda ya bayyana shi a matsayin rashin fifikon gwamnatin tarayya.

Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana aikin a matsayin zamba, wanda fadar shugaban kasa ta musanta kalaman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here