Daga: Halima Lukman.
Olubunmi Tunji-Ojo injiniyan Najeriya ne kuma ɗan kasuwa mai taimakon jama’a kuma ɗan siyasa. Kafin nada shi ministan harkokin cikin gida da shugaba Bola Tinubu yayi, ya taba zama dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Akoko na jihar Ondo daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Tunji-Ojo da yake magana a yayin ganawarsa ta farko da shugabannin hukumomin da ke karkashin kulawar ma’aikatar, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da bayar da sakamako mai kyau.
“Ina nan don yin aiki, amma a cikin aiki dole ne mu sami yanayi mai kyau. kuma wannan aikin namu ya shafi kowa, ko kai mai arziki ne ko talaka.
“Na zo nan ne domin in kawo sauyi kuma in bayar da sakamako mai kyau, kuma ina bukatar ku taimaka wajan kawo sauyi da cigaban wannan ma’aikata,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Za mu yi ƙoƙari iya bakin ƙoƙarinmu don samar da jagoranci nagari wanda kuwa zai sami hakkin sa” in ji Tunji.
A kalla kusan shekara guda kenan da karbar ragamar shugabancin ma’aikatar.
Bayan hawansa mulki, ministan ya yi gaggawar warware matsalar neman fasfo 204,000 cikin makonni biyu kacal a hukumar shige da fice ta Najeriya.
Ya kuma bullo da manhajojin masu saukin amfani da su don neman biza, tare da ba da damar yin amfani da hoton fasfo ta hanyar shige da fice da matakin da ya kara samun sauki da saukakawa ‘yan Najeriya masu neman biza.
Ga ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje kuwa, shugabancin Tunji-Ojo ya inganta wuraren fasfo na e-passport a manyan ofisoshin jakadancin Najeriya a Turai, tare da inganta iya aiki ga ‘yan Najeriya a kasashen waje irinsu Spaniya da Girka da Austreliya da kuma Italiya dadai sauransu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yaba da wannan shiri, domin a cewarsa hakan zai inganta tsaro a filayen jiragen sama na kasar tare da daukaka martabar Najeriya a duniya.
Jindadin jami’an tsaro a watan Nuwamba 2023, Tunji-Ojo ya ba da shawarar biyan albashin jami’an tsaro daidai da na ‘yan sandan Najeriya.
Ya kuma ce kamar sojoji, gwamnatin tarayya na duba yiwuwar kafa hukumar fansho na ma’aikatan hukumar shige da fice ta kasa da hukumar kashe gobara ta tarayya da jami’an tsaro da na farin kaya, da kuma hukumar gyaran fuska ta Najeriya.
Ya kuma kara da cewa hakan zai inganta ayyukan hidima da kuma rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki dangane da yadda hukumar kula da shige da fice ta kasa ta ke yi.
Wani abin sha’awa, gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Mayu, ta amince da karin kashi 25 zuwa 35 cikin 100 na albashin jami’an ‘yan sanda da sojoji da ma’aikatan gwamnati da dai sauransu.
Sai dai amma shekaru da dama, hukumomin ‘yan sanda da na soji sun kasa gina sabbin bariki ko kuma gyara wadanda ake da su yadda ya kamata.
Yayin da daya daga cikin dalilan kafa bariki shi ne magance kalubalen gidaje da ke fuskantar sojoji da cibiyoyin tsaro da masaukin baki.
Majiyoyi a cikin fadar shugaban kasa sun shaida wa SolaceBase cewa Shugaba Tinubu ya gamsu da Tunji-Ojo kuma yana fatan ganin ci gaba a ma’aikatar cikin shekaru biyu masu zuwa.