Jam’iyyar APC ta caccaki Gwamna Makinde kan kalaman da yayi na “Operation Wetie”

Oyo State Governor Seyi Makinde

Jam’iyyar APC ta yi gargadi ga Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo kan ambatar tarihin “Operation Wetie” a lokacin taron kolin jam’iyyun adawa da aka yi a Ibadan.

Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan kalaman na Gwamna Makinde.

Sakataren, ya bayyana kalaman a matsayin na tunzuri kuma mai hadari, wanda ka iya zama barazana ga tsaron ƙasa.

“Kalaman Makinde kalamai ne marasa kan gado masu barazana a fili ga zaman lafiya da tsaron kasa.”

“Abin damuwa ne matuka ace gwamna mai ci wanda tsarin mulki ya dora wa alhakin tsaron al-umma a matsayinsa na babban jami’in tsaro a jiharsa, ya fara magana akan tashin hankalin siyasa mai muni a tarihin Najeriya.” Inji sanarwar.

Ya kuma kara da cewa, jam’iyyar APC a karkashin shugabancin shugaban kasa Bola Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen karfafa tsarin dimokuraɗiyya da bin doka da oda, da kuma aiwatar da Renewed Hope Agenda domin zaman lafiya, hadin kai, da walwalar dukkan ‘yan Najeriya.

Morka ya kara da cewa ba za a yi watsi da kalaman na gwamnan a matsayin kawai maganar adawa ba, saboda hadari da hargitsi da rashin bin dokar da za su haifar, wanda zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar kasa.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da leken asiri da su dauki kalaman Makinde da muhimmanci kuma su dauki mataki don kare rayuka, dukiya, da kare tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

“Dole ne a tuna wa gwamnan cewa kariyar da tsarin mulki ya ba shi daga tuhuma ba kariya ba ce daga daukar nauyin barazana ko ayyukan da suka saba wa tsaron kasa.”

Marka, ya kuma ce babu wani mutum, komai matsayinsa, da ya mallaki ikon yin barazana ko jefa rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya cikin hadari ko rushe tsarin dimokuradiyyar da kasa ta sha wahala wajen samu da sunan zantukan siyasa.

Jam’iyyar ta APC, ta kuma sake yin watsi da kokarin shugabannin adawa na nuna matsalar cikinsu cikin labaran firgici game da abin da suke kira mulkin jam’iyya daya.

Ya kuma jaddada cewa ba za su mika wuya ga mummunar magana ba su yi watsi da aikinmu ga jam’iyyarmu ke tsarawa, da tattara jama’a don fafatawa a zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Ya kara da cewa filin dimokuradiyyar Najeriya yana da karfi yadda ya kamata, jam’iyyun siyasa kusan ashirin da suka yi rajista kuma suke shiga cikin tsarin zaben kasar cikin ‘yanci, hare-haren da barazanar da ‘yan adawa ke kai wa APC ba tare da dalili ba na tashin hankali ba komai ba ne face mika wuya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here