Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tsawaita wa’adin aiki na shekaru biyu ga shugaban ma’aikata, wasu sakatarorin dindindin, da manyan ma’aikatan gwamnati daga ranar 31 ga Disamba, 2024.
Sanarwar da Aliyu Yusuf, Daraktan Wayar da Kai na Ofishin Shugaban Ma’aikata, ya fitar ta ce, tsawaitar wa’adin ya biyo bayan gamsuwa da kwazon ma’aikatan, tare da gudun kada su bar gibin da zai iya kawo cikas ga ayyukan gwamnati.
Cikin wadanda aka yiwa karin akwai Alhaji Abdullahi Musa a matsayin Shugaban Ma’aikata, da wasu Sakatarorin Dindindin, da kuma ma’aikatan lafiya irinsu Amina Idris, Ahmad Lawan, Hussaini Nuhu, Salisu H. Nadosun, da Larai Ahmadu.
Gwamnan ya bayyana cewa, ma’aikatan sun nuna bajinta da kwarewa a aikinsu, wanda ya sa dole gwamnati ta tsawaita wa’adin aikinsu don ci gaba da tabbatar da ingantaccen gudanarwar gwamnati.